Biredin da shugaba Buhari ya yanka na bazde ɗinsa don kishin Najeriya ne

0 105

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bikin cika shekaru 79 da haihuwa yau Juma’a a birnin Satanbul na kasar Turkiyya.

Kakakin shugaban kasar mallam Garba Shehu yace  tawagar jamian gwamnati da suka yiwa shugaban kasar rakiya zuwa kasar Turkiyya ne suka shirya bikin.

Garba Shehu ya bayyana cewa yayin da Buhari ya fito daga dakinsa ya nufi dakin taro, ya gamu da jerin gwanon tawagar yan Najeriyar da wani biredi da aka yi wa kwalliya da launin tutar Najeriya.

Daga nan tawagar ta fara rera wakar taya shugaban murna.

An ce Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ya yi godiya a madadin ministocin da sauran tawagar.

Onyeama ya taya shugaban kasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yi masa fatan alheri da shekaru masu yawa a nan gaba da kuma kuzarin bautawa al’ummar Najeriya.

Da yake mayar da martani ga manema labarai, Buhari ya ce zai yi iya bakin kokarinsa ga Najeriya har zuwa ranarsa ta karshe a shekarar 2023, da zai mika mulki ga wanda zai gaje shi,

Shugaban ya kuma ce zai koma gona ne domin ci gaba noma da kiwo bayan ya miƙa mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: