Bola Ahmad Tinubu shi yafi cancanta ya mulki Najeriya a cewar Shugaba Buhari

0 71

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Sakon taya murna na shugaba Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar jiya a Abuja.

Shugaba Buhari ya kuma godewa sama da wakilai dubu 2 na jam’iyyar APC bisa yanke shawara mai kyau da ta kai ga nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Tun da farko dai shugaban kasar ya mika tutar takarar jam’iyyar APC ga Bola Tinubu.

A jawabinsa na godiya, Bola Tinubu ya godewa shugaban kasa Buhari, shugabannin jam’iyyar APC, gwamnonin da aka zaba a tutar jam’iyyar APC, wakilan jam’iyyar, masu neman tsayawa takara da duk wadanda suka taimaka wajen gudanar da taron cikin nasara.

Ya kuma jaddada bukatar hadin kai da fahimtar juna a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar domin tabbatar da nasarar zaben jam’iyyar a babban zabe mai zuwa na 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: