Bayanin da Walida Abdulhadi Ibrahim ta bayar, yarinyar da ake zargin wani jami’in Hukumar Tsaro ta DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi ya sace daga karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa, sun kara dagula shirye-shiryen mayar da ita ga iyayenta.
A wata hira ta musamman, Walida wadda yanzu ke zaune a hedikwatar DSS da ke Abuja tare da jaririyarta mai watanni uku, ta ce tana fargabar cewa iyayenta za su cutar da ita idan aka tilasta mata komawa Jigawa. Sai dai iyayenta sun karyata wannan zargi, da cewa an wanke mata kwakwalwa ne domin ta nesanta kanta da su da kuma addinin Musulunci, bayan da ake zargin Ifeanyi ya mayar da ita Kirista tare da ajiye ta a gidansa da ke Abuja.
A cikin hirar da ta yi da jaridar Weekend Trust, Walida ta ce matsalarta ta fara ne a shekarar 2023 a unguwar su dake Hadejia, inda ta zargi wata mata mai suna Mariam da sace ta tare da muzgunawa mata. Ta ce daga bisani ne aka kai ta Abuja bayan ta tsere daga gidan Mariam, kuma a nan ne ta hadu da Ifeanyi.
A nata bangaren, DSS ta ce ana tsare Walida ne domin kare lafiyarta, yayin da aka kama Ifeanyi kuma ake ci gaba da bincike a kansa. Mataimakin Darakta-Janar na DSS ya ce Walida ta nuna fargaba kan lafiyarta, kuma a matsayin hukumar tsaro, wajibi ne su kare duk wanda ya nuna tsoron barazana ga rayuwarsa.
Har ila yau, hukumar ta ce ta hada kungiyoyi daban-daban da suka hada da lauyoyin mata, kungiyoyin matasa da likitoci domin taimakawa binciken, ciki har da tantance lafiyar kwakwalwar Walida.
Mahaifin Walida, Malam Abdulhadi Ibrahim, ya musanta zargin cewa matarsa ta biyu ta gallaza wa Walida har ta gudu daga gida. Ya ce wannan labari ne da aka kirkira domin bata sunan iyalin sa.
Ya ce Walida na zaune tare da shi kafin ta bace, kuma bayan shekaru biyu da watanni biyu ana nema ba tare da nasara ba, sai wani mutum ya kira shi a waya yana sanar da shi cewa diyarsa tana Abuja, kuma ana shirin aurar da ita ga wani mutum.
Malam Ibrahim ya ce daga bisani ya gano cewa Walida ta haifi diya mace, kuma an yi mata tiyata domin haihuwar, yana mai zargin cewa an mayar da ita Kirista tare da daukar ciki tana karama. Ya kara da cewa wannan lamari ya jefa iyalinsu cikin tsananin bakin ciki, har ma mahaifiyarta ta rasu watanni uku da suka gabata saboda damuwar bacewar diyarta.
Wata kotun majistare da ke Hadejia ta bayar da umarnin kama Ifeanyi tare da gudanar da bincike kan zargin sace Walida, tsare ta ba bisa ka’ida ba da kuma tilasta mata sauya addini. Kotun ta kuma umurci DSS da ta saki Walida nan take ta mayar da ita ga iyayenta.
Sai dai DSS ta ce Walida ta zabi ci gaba da zama karkashin kulawarta saboda dalilan tsaro, kuma ta garzaya kotu domin neman a soke umarnin da aka bayar na mayar da ita ga iyayenta. Hukumar ta kuma bayyana cewa an kama jami’in da ake zargi, kuma za a dauki mataki bisa ga dokoki idan aka same shi da laifi.
Lauyan iyalan Walida ya ce bai dace DSS ta ci gaba da tsare Walida ba duk da umarnin kotu. Ya ce a Najeriya ‘yan sanda ne ke da hurumin gudanar da bincike bisa umarnin kotu, ba wata hukuma ba.
Hakazalika, wasu kungiyoyi da masu fafutukar kare hakkin bil’adama sun bukaci a bi umarnin kotu tare da tabbatar da an gudanar da bincike cikin gaskiya. Kungiyar mata Musulmi ta Najeriya ta bukaci a saki Walida nan take tare da mayar da ita ga iyayenta, tana mai cewa dole ne a tabbatar da adalci.