Cutar Sankarau a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta kashe fiye da mutane 120

0 96

An bayyana bullar Cutar Sankarau a Jamhuriyar Demokradiyar Congo wanda ta kashe mutane 120 kawo yanzu.

Kawo yanzu kimanin mutane 100 ne suke cigaba da samun kulawar likitoci a cibiyoyin lafiyar kasar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce zai yi wahala a iya dakile cutar saboda yankunan da cutar ta bulla sun yi amanar cewa Maitace.

Hukumomi sun dora karuwar cutar kan rashin daukar matakan da suka kamata tun da farkon bullar cutar.

A cewar Masana kan fannin Lafiya, maimakon daukar matakai, mutanen suna sauya wurare daban-daban bisa tunanin cutar bazata bisu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: