Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da bude makarantun firamare da sakandare

0 51

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da bude makarantun firamare da sakandare a fadin Jihar daga ranar Lahadi, 12 ga Satumba, 2021.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a yau Alhamis ta ce bayan bude makarantun za su koma ne a matsayin zangon farko na shekarar karatu ta 2021/2022, An tsallake zango na uku da ya kamata su koma.

Jadawalin shekarar karatun da gwamnatin ta fitar ya nuna cewa za a kammala zangon na farko a ranar 15 ga watan Disamba, 2021 sannan a dawo zango na biyu a ranar 9 ga Janairu, 2022.

Hakan na zuwa ne bayan sau biyu gwamnatin na dage dawowar makarantun a watan Yuli, bayan hutun suka tafi na zango na biyu.

Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Dokta Shehu Muhammad ya shine ya shaida hakan a wani taro inda yace, gwamnatin za ta fitar da tsarin amfani da intanet, domin cike zangon karatu na uku da aka tsallake.

Ya kuma bayyana cewa makarantun za su fara komawa a ranar da aka ayyana din ne a rukuni-rukuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: