Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa ta na bincike kan harbin da aka yiwa matar kwamishina a jihar Katsina

0 82

Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa reshen Jihar Katsina ta kafa kwamatin da zai binciki zargin da Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi na Jihar Hon Yau Umar Gwajo-Gwajo ya yi na cewa Jami’an hukumar sun harbi motar sa.

Manema Labarai sun rawaito cewa Alhaji Umar Gwajo-Gwajo ya yi zargion cewa Jami’an hukumar ta Customs sun budewa motar sa wuta a ranar Talata, a lokacin da yake kan hanyarsa ta barowa karamar hukumar Mai Aduwa.

Sai dai Kwamashinan ya yi nasarar tsallake Harbin da Customs suka masa, amma sun sami Motarsa.

Mukaddashin Kwanturolan hukumar ta Custom reshen Jihar Katsina Malam Dalha Wada Chedi, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da kwamatin.

A cewarsa, yana da tabbacin cewa kwamatin zai yi adalci wajen gudanar da binciken sa, tare da gabatar da rahoto.

A wani labarin kuma, rundunar hukumar ta kama kayayyaki wanda darajar kudin su ya kai Naira Miliyan 65 cikin wata 1.

Mista Chedi ya ce daga cikin kayayyakin da hukumar ta kama sun hada da Shinkafa yar kasar waje, da Katan din Kuskus, da Madara da Cylinder ta Gasa da kuma Taliya ta Spaghetti.

Sauran kayayyakin da hukumar ta kama sun hada da Mota kirar Mercedes Benz, da Peugeot 504 da kuma Toyota Hilux da kuma Nissan.

Kazalika, ya ce hukumar zata yi duk mai yuwuwa domin dakile safarar haramtattun kayayyaki zuwa kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: