Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci zababbun Shugabannin Kananan hukumomi 27 da su gudanar da shugabanci nagari

0 71

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci zababbun Shugabannin Kananan hukumomi 27 na jihar nan, su gudanar da shugabanci Nagari tare da gaskiya da amana, kamar yadda yake cikin kudin tsarin mulkin kasa.

Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi na Jihar Jigawa Hon Kabiru Hassan Sugungum, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wurin bawa sabbin shugabannin kananan hukumomin da mataimakan su da kuma Kamsilolin kananan hukumomi 27 horo kan sanin makamar aiki.

A cewarsa, an shirya taron horaswar ne domin bada horo ga Mahukuntan kananan hukumomi, kan tanajin kudade da shugabanci nagari da kuma bin doka da oda.

Kwamishinan, ya ce taron zai kuma sake bawa shugabannin kananan hukumomin dabarun aiki da kuma yadda ayyukan kananan hukumomi suke a kundin tsarin mulkin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: