A kalla mutane 39 ne suka mutu biyo bayan ambaliyar ruwa da Gobara a kananan hukumomin Guri da Kafin Hausa

0 99

A kalla mutane 39 ne suka mutu biyo bayan ambaliyar ruwa da Gobara a kananan hukumomin Guri da Kafin Hausa da kuma Malam Madori na Jihar Jigawa.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa SEMA, Alhaji Yusuf Sani Babura, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Ofishinsa, inda ya ce ambaliyar ruwan da aka samu a cikin Guri ta shafi 1 bisa 3 na mutanen garin tare da lalata garuruwa 400 da kuma kashe mutane 10.

Haka kuma ya ce ambaliyar ta rushe gidaje dubu 1000 a biranen Taura da Ringim da Birnin Kudu da kuma birnin Dutse da wasu kananan hukumomin da suke jihar nan.

Sakataren Zartarwa na hukumar, ya ce a kwanan nan ne wata Mota wanda ta dauko Fasinjoji 29 daga Gumel tayi hadari tare da kamawa da wuta a Shuwarin, babu mutum daya da ya rayu daga cikin fasinjojin, inda ya ce hukumar ta bada Naira dubu 100,000 ga Iyalan Matatan.

A cewarsa, ambaliyar ruwan da aka gudanar a shekarar bara ta shafi kananan hukumomi 18 daga cikin 27 da suke fadin jihar nan, inda hukumar ta bada kayan agaji na Naira Biliyan 2.

Alhaji Yusuf Babura, ya ce hukumar ta bada kayan abinci da mayafai da magunguna da kuma katifu ga mutanen da suka gamu da iftila’in.

Kazalika, ya ce shawarci mutanen da suke zaune kusa da Magudanan ruwa su rika tsaftace muhallansu da kuma magudanan ruwa domin dakile ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: