Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta koka kan halin da fannin Ilimin Jihar yake ciki

0 68

Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta koka kan halin da fannin Ilimin Jihar yake ciki.

Shugaban Kwamatin Ilimi na Malisar Dokokin Jihar Hon Babayo Akuyum, shine ya bayyana hakan a lokacin da ake kaddamar da Sakatarorin Ilimi na kananan hukumomi 20 da suke Jihar, wanda Hukumar Ilimi a Matakin Farko ta jihar tayi.

Hon Akuyum, ya ce gwamnatin Jihar bazata lamunci mummunan yanayin da Ilimin Jihar yake fuskantar ba, wanda hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta dauki gabaran gyara fannin.

Dan Majalisar ya bukaci sabbin sakatarorin Ilimin su kasance masu jajircewa a ayyukan su, tare da sanya idanu kan Malaman Makarantun da suke Jihar ta Bauchi.

Shima a Jawabinsa, Sakataren Zartarwa na hukumar Ilimi a Matakin Farko na Jihar Bauchi Dr Abubakar Sirimbai, ya ce an zabo sakatarorin ne bisa cancantar su, inda ya bukaci suyi amfani da damar da aka basu wajen ciyar da jihar gaba.

Kazalika, ya bukaci su kasance masu gaskiya da amana a lokacin da suka gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: