Wani Sufetan yansanda ya harbe wani Sajan biyo bayan wata sa’insa a tsakaninsu a jihar Kano

0 100

Wani Sufetan Yan Sanda wanda yake aikin a rundunar Yan sandan Jihar Kano mai suna Ya’u Yakubu, ya harbe wani Sajan mai suna Basharu Alhassan, biyo bayan wata sa’insa a tsakaninsu.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare a karamar hukumar Warawa ta Jihar Kano, bayan fada ya kaure a tsakanin su.

Manema Labarai sun rawaito cewa a lokacin fadan Sufeta Ya’u Yakubu ya yi amfani da bindigar sa, inda ya harbe Sajan Basharu Alhassan.

Bayan faruwar lamarin ne Yan Sanda suka dauki Sajan din zuwa babban Asibitin Kwantarwa na Wudil, inda Likitoci suka tabbatar musu da mutuwar sa.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Manema labarai.

A cewarsa, Lamarin ya faru ne bayan Marigayin ya yi Sufeta Yakubu dariya sakamakon sauyin wurin aiki da aka masa zuwa kyauyen Warawa.

Kazalika, ya ce Kwamishinan Yan sandan Jihar CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bada umarnin cigaba da bincike a babban ofishin hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: