Gwamnatocin Najeriya sun maka gwamnatin tarayya kara a kotu bisa kin biyansu kudaden da ake samu na haraji

0 97

Gwamnatocin jihoshi 36 na kasarnan sun maka gwamnatin tarayya kara a kotu bisa zargin kin biyansu kudaden da ake samu na harajin hada-hadar kudade da ake kira stamp duty.

Gwamnatocin jihoshin karkashin manyan lauyoyinsu, sun shigar da karar babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, wanda yake wakiltar gwamnatin tarayya.

Sun bukaci kotun ta umarci gwamnatin tarayya ta biya kudi sama da naira biliyan 176 da ta karba a matsayin harajin daga hada-hadar kudaden daidaikun mutane a jihoshinsu daga shekarar 2015 zuwa 2020.

Sun yi ikirarin cewa gwamnatocin jihoshi ne suke da karfin ikon karbar harajin ba gwamnatin tarayya ba.

Karar na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin jihar Rivers take kiki-kaka a shari’ah tare da gwamnatin tarayya dangane da kudaden harajin kayayyaki (VAT).

A ‘yan kwanakinnan, babbar kotun tarayya dake Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, ta yanke hukuncin da ya marawa jihar baya, matakin da tuni gwamnatin tarayya ta daukaka kara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: