Rundunar sojin Najeriya tace dakarunta sun cafke wani babban kwamandan Boko Haram a jihar Borno

0 73

Rundunar sojin Najeriya tace dakarunta sun cafke wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Yawi Modu, wanda a ‘yan kwananan aka ayyana nemansa ruwa a jallo.

Cikin wata sanarwa jiya a Abuja, kakakin sojoji, Birigediya Janar Onyema Nwachukwu yace dakarun sojin sun kuma wawashe kayayyakin hada bama-bamai a jihoshin Borno da Yobe.

Dakarun sojin sama da shekaru 5 baya suka ayyana neman mayakan Boko Haram sama da 100 ruwa a jallo. Kazalika ta kuma wallafa hotunansu a bainar jama’a.

Kamen kwamandan yazo ne daidai lokacin da mayakan Boko Haram ke tuba su mika wuya tare da iyalansu ga hukumomi.

Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun addabi yankin Arewa maso Gabas da na tafkin Chadi cikin sama da shekaru 10.

Sanarwar Nwachukwu tace sojojin sun kwato buhunan takin zamani sama da 100, wanda gwamnatin tarayya ta haramta a ‘yan kwanakinnan saboda yadda ake hada bama-bamai da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: