Gwamnatin Jihar Jigawa zata samar da iskar taimakawa numfashi yara ‘yan kasa da shekaru 5 masu fama da ciwon sanyi

0 95

Gwamnatin Jihar Jigawa tace yara ‘yan kasa da shekaru 5 masu fama da ciwon sanyi na lumoniya da sauran cutuka, zasu samu iskar taimakawa numfashi ta oxygen a kyauta.

Daraktan Lafiyan Jama’a a ma’aikatar lafiya ta jiha, Dr. Abdullahi Namadi, ya sanar da haka jiya a Birnin Dutse.

Yace matakin ya biyo bayan kokarin gwamnatin jihar wajen aiwatar kudirin lafiya na kasa akan iskar taimakawa numfashi ta oxygen a jiharnan.

Ya kara da cewa mata masu juna biyu suma sun cancanci amfani da iskar taimakawa numfashi ta oxygen a kyauta.

Yayi bayanin cewa idan kudirin ya tabbata, yara ‘yan kasa da shekara 5 da mata masu juna biyu za suke samun iskar taimakawa numfashi ta oxygen a kyauta.

Abdullahi Namadi ya kara da cewa ma’aikatar lafiya ta jiha tana kuma aiki wajen sanya iskar taimakawa numfashi ta oxygen a cikin magungunan da ake bayarwa a shirin inshorar lafiya na jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: