Dalilan da yasa jirgin saman rundunar soji yayi hatsari a Zamfara

0 81

Wani jirgin saman rundunar sojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan da ƴan fashi suka buɗe masa wuta.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ranar Litinin ta ce matukin jirgin mai suna Laftanal Abayomi Dairo, ya tsira da ransa.

Jirgin yana komawa ne bayan da ya kammala wani aiki mai cike da nasara a tsakanin iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.

Bayan da ya tsira daga faɗuwa daga jirgin sai kuma ƴan bindigar suka buɗe masa wuta, amma ya samu sa’ar kauce musu ya kuma nemi mafaka a wani ƙauye har zuwa wayewar gari.

Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin da aka samu labarin hatsarin, sai Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Oladayo Amao, ya bayar da umarnin cewa a yi duk ƙoƙarin da za a yi don ceton matuƙin.

Rundunar sojin sama ta ce mako biyu kenan tun sanda ta fara kai samame ta sama ba dare ba rana a maɓoyar ƴan bidniga, biyo bayan umarnin da Shugaba Buhari ya bayar cewa a zaƙulo su duk inda suke a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: