Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya koka da hauhawar farashin kayan Masarufi a Kasuwanni, inda ya ce kara farashin kayan Masarufin baiyi daidai da koyarwar addinin Musulunci ba.

A sakon sa ga yan Najeriya kan murnan bikin Sallah Layya, Shugaba Buhari, ya bukaci Musulmai su nuna kyawawan halayya na koyarwar Addinin Musulunci.

Haka kuma ya ce gwamnatinsa zata cigaba da samar da kyakkyawan yanayi tare da kare rayuka da Dukiyoyin yan Najeriya, kamar yadda yayi Alkawari.

Da yake jawabi kan kalubalan da suke addabar kasar nan, Shugaba Buhari ya ce Cutar Corona ta shafi tattalin arzikin Kasashen Duniya ciki harda Najeriya, kari akan ta’adin da ambaliyar ruwa ta yiwa Manoma tare da lalata gonakan su.

Kazalika, Shugaba Buhari ya ce matsalolin tsaro, wanda suka hada da hare-haren yan Bindiga da masu Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma masu ikirarin Jihadi, ya shafi Abincin da Kasar take Nomawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: