‘Yansanda sun kama mutane 10 da laifin yahu-yahu a Kano

0 122

Rundunar Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Kano, ta kama mutane 10, bisa zargin su da aikata laifukan Cirar kudade a Asusun bankunan Mutane ba tare da sanin su ba.

Matasan da aka kama din sun hada da Umar Aminu, Muhammad Muhammad, Kabiru Idris, Salim Sani, Umar Muhammad, Yusuf Ibrahim, Aminu Lawan, Jibril Aliyu, Hauwa Abubakar and Aisha Abubakar (two female and eight males) kuma na kama su ne a wani Otal dake cikin birnin Kano.

Cikin wata sanarwar da Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai a Kano, ya bayyana cewa Matasan sun shahara wajen cirewa mutane kudade a Asusun su, ba tare da sanin su ba.

Kakakin rundunar, ya ce Matasan sun amsa aikata laifukan da ake zargin su, tare da Cire kudade masu tarin yawa.

A jawabinsa, Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano Malam Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bada umarnin a cigaba da gudanar da bincike, inda ya kara da cewa za’a gurfanar da mutanen a gaban Kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: