Kimanin Mutane 30 ne Cutar Kwalara ta Kashe a nan jihar Jigawa, a Cewar Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Dr Salisu Mu’azu.

Da yake zantawa da manema Labarai a Ofishinsa, Babban Sakataren ya ce kimanin mutane dubu 2,000 ne suka harbu da cutar Kwalara a fadin jihar nan, inda kuma ta hallaka mutane 30.

A cewarsa, an samu bullar cutar ne cikin Kwanaki 30, inda ta bulla a kananan hukumomin Ringim da Dutse da Hadejia da Kirikasamma da kuma Birnin Kudu.

Dr Salisu Mu’azu, ya ce cutar tafi tsanani a kananan hukumomin Dutse da Hadejia, sakamakon yin amfani da ruwan Rijiya da na Kogi a gidajen su sabanin mai tsafta.

Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiyar, ya ce Kwalarar ta sake tsananta, saboda Mamakon ruwan Sama, wanda ya kwasho abubuwan da zai iya zama Cuta, tare da shiga cikin Magodanan ruwan da Mutane suke sha.

Haka kuma ya ce Gwamnatin jihar nan ta umarci a kai Magunguna a Cibiyoyin da ta ware guda Uku a Kanana hukumomin Hadejia da Dutse da kuma Ringim, a kokarin da gwamnatin jiha take yi wajen dakile matsalar.

Kazalika, ya ce Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da Gidauniyar Likitoci Masara Shinge sunyi hadin gwiwa da gwamnatin jiha domin dakile matsalar akan lokaci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: