Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya litinin, ya nanata kudurin gwamnatinsa, na fitar da yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin talauci, inda ya kara da cewa hakan zai yuwu matukar an samu samu hadin gwiwa tsakanin Gwamnati ta mutane.

Da yake jawabi a lokacin da yake kaddamar da Gandun Gonar Hukumar Bunkasa Kasa ta Fannin Noma wanda ita ce ta farko da aka kaddamar a karamar hukumar Daura ta Jihar Katsina, Shugaba Buhari ya ce Dogaro da Mai na Cigaba da durkusa kasar nan fiye da shekaru.

Shugaba Buhari ya ce tattalin Arzikin Najeriya ya Dogara ne Kacho kan akan Fannin Noma a yanzu, musamman ganin yadda Matasa ke cigaba da samun damarmakin a fannin Noma da Kiwo.

Kazalika, shugaba Buhari, ya ce Najeriya zata cigaba da taka muhimmiyar rawa a fannin Noma, domin sake inganta Noman Abinci da Kiwon Dabbobin Gida domin samarwa Matasa ayyukan yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: