Kimanin mutane 146 ne suka harbu da cutar Corona a Najeriya a jiya Litinin

0 70

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane 146 ne suka harbu da cutar Corona a Najeriya a jiya Litinin.

A cewar NCDC an samu bullar cutar Corona a jihohi 5 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Cibiyar dakile cututtuka ta NCDC ta ce a jihar Lagos (134), Ondo (3), Cross River (2), FCT (2), Kwara (2), Ogun (1), Oyo (1), Rivers and (1).

Haka kuma cibiyar ta ce an sallami mutane 11 a jiya, bayan sun warke daga cutar, inda kuma aka samu karin mutum 1 da cutar ta hallaka.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 164, 678 ne suka samu da cutar a Najeriya tun bayan bayyanar cutar a Najeriya, haka kuma cikin adadin kimanin mutane dubu 164,710 ne aka sallama daga cibiyoyin kula da masu cutar a kasa baki daya.

Kazalika kimanin mutane dubu 2,128 ne cutar Corona ta hallaka a kasar baki daya.

Cibiyar NCDC ta ce a yanzu haka akwai kimanin mutane dubu 2,800 da suke cigaba da samun kulawar likitoci a cibiyoyin da aka ware musu a kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: