Yan Bindigar da suka sace Dalibai 121 na Makarantar Sikandiren Bethel dake Jihar Kaduna, sun bukaci Naira Miliyan 60 kafin sakin Daliban.

Yan Bindigar sun sace Daliban ne su kimanin 100 a ranar wata Litinin data gabata.

Shugaban Makarantar Rev Ishaya Jangado, ya ce bayyana gudanar da kididdiga sun gano cewa kimanin daliban 121 ne yan bindigar suka sace kuma suke tsare dasu.

A jiya litinin Manema labarai sun gano cewa yan Bindigar sun bukaci biyan Naira dubu 500,000 kan kowanne Dalibi cikin daliban da suka sace.

An rawaito cewa yan bindigar sun bawa gwamnatin wa’adin litinin domin a biya kudin fansar, bayan yan bindigar sun saki Dalibi daya saboda dalilai na rashin lafiya.

Wata majiya da ta fadawa manema labarai cewa Choci da Iyayen Daliban sun kokarin wajen hada kudaden fansar kamar yadda suka bukata.

Kazalika, majiyar ta ce yan bindigar sunyi Alkawarin sakin daliban a a yau Talata matukar an biya kudin fansar kamar yadda suka bukata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: