Dalilin da Ya Sa Aka Kashe Murtala Muhammed

0 337

A’isha Muhammed, ’yar tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammed, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka kashe mahaifinta.

A cewar A’isha, rayuwar sauƙi da mahaifinta ke yi da kuma tsayayyen salon jagoranci ba tare da sassauci ba ne suka sa ya zama mai sauƙin kai masa hari har aka kashe shi.

Da take magana a shirin Morning Show na ARISE News ranar Litinin, yayin da Najeriya ke tunawa da cikar shekaru 50 da rasuwar marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed, A’isha ta waiwayi dabi’u da akidun mahaifinta, tana bayyana shi a matsayin shugaba da ke aikata abin da yake faɗa.

A cewarta, Janar Murtala Ramat Muhammed ya kasance mai tsananin jajircewa wajen riƙon amana, ɗaukar alhaki da ladabi, kuma yana kallon cin hanci da rashawa a matsayin babbar barazana ga al’umma.

“Ina ganin salon jagorancinsa a bayyane yake. Yana jagoranci da tsari. Ya yi imani da riƙon amana. Ya yi imani da ɗaukar alhaki,” in ji ta.

A’isha ta ce mahaifinta bai tsaya kawai yana magana kan yaƙi da cin hanci ba, har ma rayuwarsa gaba ɗaya ta kasance ta ƙin cin hanci, tana mai jaddada cewa yana kallon rashawa a matsayin “ƙwari mai cin jiki” da ke iya lalata ƙasa.

“Dukkanmu mun san matsayinsa kan yaƙi da cin hanci. Ba magana kawai yake yi ba… bayan shekaru 50, ku dubi abin da ya faru,” ta ƙara da cewa.

Ta kuma bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasar ya ƙi jin daɗin mulki da shagulgula, inda bai yarda da dogayen jerin motoci, amo na jiniya, ko tsauraran matakan tsaro ba, yana son ya rayu kamar talakan ɗan Najeriya.

“Mahaifina bai kasance yana yawo da jerin motoci da jiniya ko tsaro mai yawa ba. Hakan ne halayyarsa,” in ji A’isha.

A cewarta, wannan sauƙin rayuwa ne ya sa ya zama mai sauƙin kashewa a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

“Shi ya sa aka samu sauƙin kashe shi. Bai kasance da tsaro mai yawa tare da shi ba.

“Yana cikin cunkoson ababen hawa kamar kowa,” in ji ta, tana ba da labarin yadda jami’an kula da hanya suka tsaida shi kafin masu kai harin su buɗe masa wuta.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya hau mulki ne ta hanyar juyin mulki ba tare da zubar da jini ba a watan Yuli 1975, wanda ya kifar da gwamnatin Janar Yakubu Gowon, amma aka kashe shi bayan kusan watanni shida kacal a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Duk da gajeren lokacin mulkinsa na kwanaki kusan 200, ana tunawa da shi saboda manyan sauye-sauye da ya aiwatar, ciki har da korar fiye da ma’aikatan gwamnati 10,000 bisa zargin cin hanci, ƙirƙirar sabbin jihohi bakwai, da kuma fara shirin komawa mulkin farar hula.

Haka kuma, gwamnatinsa ce ta aza harsashin matsar da babban birnin ƙasa daga Legas zuwa Abuja.

Leave a Reply