NAHCON Ta Kammala Kama Masaukin Mahajjata A Makkah da Madina

0 173

Hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya, NAHCON ta ce ta samu nasarar kammala kama masaukin mahajjatan ƙasar kafin wa’adin da ƙasar Saudiyya ta saka.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban hukumar kan harkokin watsa labarai, Ahmad Muazu ya fitar a madidin shugabanta.

A sanarwar, ya ce shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne sanar da kammala duk wani shirye-shirye da suka shafi kama masauki.

“Najeriya ta samu nasarar kammala kama masaukin ne a Makkah da Madina tun kafin ranar da ƙasar Saudiyya ta ware domin kammala duk abubuwan da suka shafi masaukin mahajjata.”

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar na aiki ne bisa umarnin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya buƙaci hukumar ta Najeriya ta riƙa kallama shirye-shiryenta kafin wa’adin ƙasar Saudiyya.

Leave a Reply