Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki a shirye take ta karɓi tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, idan ya yanke shawarar shiga APC.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Trust TV a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, biyo bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya jawo wasu ƴan Majalisar Dokokin Jiha da na Majalisar Wakilai su bi sahunsa.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa APC na ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar a Jihar Kano, wacce ake ganin tana daga cikin jihohin da za su taka muhimmiyar rawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar ya kuma kare yawan tafiye-tafiyen ƙasashen waje da Shugaba Bola Tinubu ke yi, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa matsayin Nijeriya a idon duniya da jawo zuba hannun jari. Ya jaddada cewa tafiye-tafiyen na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa haɗin gwuiwar tsaro tsakanin Nijeriya da ƙasashen waje.