Darakta-Janar na Hukumar NITDA ya ce yin zabe ta hanyar amfani da internet ya zama wani muhimmin al’amari na gudanar da mulkin dimokaradiyya

0 88

Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA, Kashifu Inuwa, a jiya, ya ce yin zabe ta hanyar amfani da internet ya zama wani muhimmin al’amari na gudanar da mulkin dimokaradiyya mai amfani da fasahar sadarwa, wanda ke kawo ci gaba.

Kashifu Inuwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da kasida a wani taron gudanar gwamnati ta intanent a Najeriya na bana a Abuja.

Kashifu Inuwa ya samu wakilcin mukaddashin daraktan sashen cigaban gudanar gwamnati ta intanent na hukumar, Bernard Ewah.

Darakta-Janar na NITDA ya ce fasahar zabe ta intanet zata tallafawa daya ko sama da haka daga cikin manyan matakai na tsarin zabe, tun daga matakin rajista da gabannin kada kuri’a zuwa zabe, da jefa kuri’a a akwati da tantancewa zuwa kidaya ko tattara sakamako bayan zabe.

Ya kuma ce, gudanar da mulki ta intanet ya zama muhimmiyar hanya wajen inganta shigar da ‘yan kasa, sa ido da kuma tantance ayyukan gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: