Dattawan Arewa sun bayya na cewa ba wanda zai marawa ko wana dan takara baya a zaben 2027

0 493

A wani labarin kuma, kungiyar dattawan Arewa wato ACF, ta bayyana cewa yankin Arewa ba zai marawa kowane dan takara baya a zaben 2027 ba, sai wanda ya nuna himma da jajircewa wajen kare muradun yankin.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, ne ya bayyana hakan a wani taron kwamitin da ya gudana a Kaduna, inda ya bayyana cewa Arewa na da karfin siyasa da adadin jama’a da zai bata damar zama jagora idan har ta hada kai.

Ya ce Arewa na da jihohi 19 da birnin tarayya, da rinjaye a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, da kuma cikin sauran manyan kwamitoci na kasa, wanda hakan ya isa ya tabbatar da karfin yankin.

Kungiyar ta ACF ta kuma yi gargadin cewa duk wani yunkurin kamfen din wur-wuri domin 2027 na iya dagula akalar mulki, tare da sanar da shirin kafa wani kwamiti da zai duba ayyuka da manufofin gwamnati domin tantance ko an bai wa Arewa hakkinta yadda ya kamata.

Leave a Reply