Yau ce ranar Ma’aikata ta duniya a Nijeriya

0 481

A yau ne ma’aikatan Najeriya ke bikin ranar Ma’aikata ta duniya, amma kungiyar kwadago ta kasa NLC da takwararta TUC sun bayyana bakin cikin yadda halin rayuwa ke ci gaba da dagulewa ga ma’aikata a kasar.

Daga Jihar Bayelsa zuwa Imo, da Oyo da Ebonyi, shugabannin kungiyoyin sun bayyana yadda karin albashi mafi karanci na Naira dubu saba’in da aka sanar ya zama marar amfani, la’akari da hauhawar farashin kaya da karancin kudin shiga.

Sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da kara dagula al’amura tun bayan cire tallafin man fetur da kuma faduwar darajar Naira, lamarin da ya haddasa hauhawar farashi da galabaita rayuwar ma’aikata a fadin kasar nan.

Sai dai a wani bangare, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Majalisar Dokoki da bangaren zartarwa za su hada kai domin warware matsalolin ma’aikata tare da samar da ci gaba da walwala.

Leave a Reply