Dimokuraɗiyya Na Amfanar Masu Mulki Fiye Da Talakawa — Hakeem Baba-Ahmad

0 203

Shugaban Jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmad, ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya ta fi amfanar masu riƙe da madafun iko, yayin da mafi yawan ƴan ƙasa ke ci gaba da fama da talauci da rashin tsaro.

Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ta gaskiya ita ce wadda ke bai wa jama’a damar zaɓar shugabanni nagari da kuma sauya waɗanda suka gaza.

Haka kuma, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi amfani da ƙuri’arsu wajen kawo sauyi da inganta rayuwar al’umma.

Leave a Reply