Barau Jibrin Ya Kafa Tarihi Da Gabatar da Ƙudurori 42 Cikin Shekaru Uku A Majalisar Dattawa

0 170

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya zama ɗan majalisar da ya fi kowa gabatar da ƙudurorin ƴan majalisa a Majalisar Dattawa ta 10, bayan gabatar da jimillar ƙudurori 42 tsakanin Yuni 2023 zuwa Yuni 2026.

Bayanan da mujallar The Parliamentarian ta fitar yayin bikin cikar Majalisar Dattawa shekaru uku sun nuna cewa guda biyar daga cikin ƙudurorin sun riga sun zama doka, yayin da sauran ke ci gaba da bin matakan majalisa.

Ƙudurorin da Sanata Barau ya gabatar sun shafi fannoni da suka haɗa da ilimi, lafiya, noma, tattalin arziki, makamashi, tsaro da gyaran kundin tsarin mulki.

A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, wannan nasara na nuna ƙwarewa da jajircewar Sanatan Kano ta Arewa wajen gudanar da ayyukansa duk da nauyin jagoranci da yake ɗauke da shi a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Dokokin ECOWAS.

Leave a Reply