Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce dole ne gwamnatoci a kowane mataki su kara saka hannun jari a makarantun gwamnati domin inganta harkar ilimi a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne a babban taron kacici-kacici na kasa na bana da Cibiyar Nazarin Majalisun dokoki da Dimokaradiyya ta kasa ta shirya, wanda aka gudanar jiya a Abuja.

An dai shirya gasar ne ga makarantun sakandire dake fadin babban birnin tarayya da kuma shiyyoyin kasarnan guda shida.

A jawabinsa, Ahmad Lawan ya ce dole ne a kara zuba jari domin inganta makarantun gwamnati a fadin kasar nan.

Ahmad Lawan yayin da yake jaddada muhimmancin ilimi, ya ce ilimi musamman a matakin farko da kuma a matakin sakandire dole ya zama tilas kuma kyauta ga dukkan ‘yan kasa.

Ahmad Lawan ya ce Cibiyar Nazarin Majalisun dokoki da Dimokaradiyya ta kasa tana amfani gasar ta kacici-kacici wajen wayar da kan jama’a, da ilimintar da su da fahimtar da su tarihi da da ayyukan majalisun dokokin Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: