An sanyawa wani titi sunan Muhammadu Buhari saboda karrama shugaban kasar Najeriya

0 61

Fadar shugaban kasa a jiya ta ce sanyawa wani titi a jamhuriyar Nijar sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari alama ce da ke nuna irin girmamashi da makwabtan na Najeriya ke yi masa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan a Yamai babban birnin kasar Nijar jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani babban titi da aka sanyawa sunansa.

Garba Shehu ya ce Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, tare da rakiyar magajin garin Yamai da sauran jami’ai, sun dauki shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa rangadi a titin mai tsawon kilomita 3.8 wanda aka kaddamar da shi bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Hadimin shugaban kasar ya ruwaito shugaban kasa Muhammad Buhari yana nuna jin dadinsa da alakar da ke tsakanin Najeriya da makwabtanta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana imanin cewa irin wannan alaka ta taimaka matuka, musamman a fannin magance matsalar tsaro a kan iyakokin kasar, da shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma fasa kwauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: