DSS ta kamo wadanda ta ce suna shirya gwamnatin wucin gadi – Yabagi Sani

0 112

Shugaban majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC), Alhaji Yabagi Sani, ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo wadanda ta ce suna shirya gwamnatin wucin gadi.

Sani ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s a shirin Politics Today.

Hukumar ta DSS a jiya Laraba ta bayyana cewa wasu manyan ‘yan siyasa na shirin kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar nan.

Amma a cikin hirar Sani ya ce, Idan har  hukumar ta DSS) sun san cewa mutum yana wani abu da bai dace da dimokuradiyya ba don tada zaune tsaye, wanda yace abin da ya dace a tsare mutumin a yi masa tambayoyi. Amma yin wannan furci zai ƙara haifar da tashin hankali ko rikici a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: