Dubban gidajen mai na ci gaba da rufewa a arewacin Najeriya

0 243

Dubban gidajen mai a Najeriya na ci gaba da dakatar da sayar da mai a sassa daban-daban a yankin arewacin ƙasar, sakamakon ƙaruwar asarar kuɗaɗe da suka ce suna yi.

Masu gidajen mai sun bayyana cewa rashin tabbas ko yawan sauyawar farashi da sauran matsaloli ne ke tilasta musu ɗaukar matakin.

Abdullahi Idris, mataimakin shugaban ƙungiyar masu samar da mai da gas ta Najeriya, wato NOGASA ya shaida wa BBC cewa mafi yawan gidajen man arewacin Najeriya ba sa iya cin riba, sai dai faɗuwa.

Ana sayo mai daga Legas kan naira 835, ko 840 a kan kwace lita, sannan ka biya kuɗin mota, kowace lita a kan naira 50 zuwa Abuja, ko 55 zuwa Kano da Kaduna, to za ka ga farashin ya ƙure, ribar ba ta wuce naira 10, in ji shi.

”To wannan naira 10 kuma idan ka haɗa galibi ba ta wuce naira 500,000, to idan wani aikin gyara ya taso a gidan mai, kuma ka biya kuɗin sauran hidimomin gidan mai, sai ka ga ta ƙare”, kamar yadda ya bayyana.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ta NOGASA ya ce a kudancin Najeriya ba a fuskantar wanann matsalar, saboda masu saro man ba su da yawa, kuma kuɗin motarsu bai fi naira 15 ba, don haka suna samun ribar fiye da naira 100, saɓanin arewa.

Leave a Reply