Babban Lauyan Gwamnati da EFCC sun karyata zargin da ake musu na shawo kan ‘yan adawa dan su sauya sheka

0 186

Ofishin Babban Lauyan Gwamnati da Hukumar EFCC sun karyata zargin cewa sun yi ganawar sirri da wasu gwamnoni ‘yan adawa domin shawo kansu su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Wadannan zarge-zarge sun fito ne daga bakin Paul Ibe, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV, inda ya ce gwamnatin Tinubu na amfani da hukumar EFCC don murkushe ‘yan adawa.

Sai dai mai magana da yawun Ministan Shari’a, Kamarudeen Ogundele, ya ce wannan zargi ne kawai kuma babu wata hujja da ke tabbatar da hakan. EFCC ta kuma fitar da wata sanarwa inda ta ce shugabanta, Ola Olukoyede, ba ya nuna bambancin jam’iyya kuma yana bin doka ne kawai yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da wadannan zarge-zargen da ya ce “kirkirarru ne kawai domin bata sunan gwamnatin.”

Leave a Reply