Lokaci ya yi da PDP za ta tattauna da Peter Obi domin dawo da shi cikin jam’iyyar – Segun Sowunmi

0 214

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya bayyana cewa lokaci ya yi da jam’iyyar za ta tattauna da Peter Obi domin dawo da shi cikin jam’iyyar.

A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Sowunmi ya ce Obi wanda ya taba zama dan jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u sama da miliyan shida a zaben 2023, yana mai cewa PDP ta rasa zabe ne saboda rashin iya cin moriyar irin wannan karfi daga yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce rashin tsari da sauya sheka da dama zuwa APC duk sakamakon matsalolin cikin gida ne, ba laifin abokan hamayya ba.

Sowunmi ya kara da cewa ‘yan PDP da ke daukar Bola Tinubu a matsayin marar karfi sun manta cewa duk da tsufarsa, yana da hazaka matuka, yana mai cewa kuskure ne a ci gaba da daukar jam’iyyar APC da shugabanta a matsayin mai saukin kayarwa a siyasance.

Leave a Reply