EFCC na da ikon ci gaba da bincike kan zargin badakalar filin da ya kai naira biliyan 3.5 – Babban Kotun Kano

0 151

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukunci cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC, na da ikon ci gaba da bincike kan zargin badakalar filin da ya kai naira biliyan 3.5, wanda ya shafi wasu fitattun malamai a jihar.

A cewar rahotannin daga manema labarai, malamai sun shigar da kara kotu domin hana kama su bisa zargin sayar da wani fili da aka ware domin gina cibiyar karatun Alkur’ani ga wata kamfani ta kashin kai ba bisa ka’ida ba.

Alkalin kotun, Musa Shuaibu, ya yi watsi da karar nasu tare da dora musu tara ta naira dubu dari biyu da hamsin bisa laifin bata lokacin kotu, yana mai bayyana cewa EFCC tana da hurumin da kundin tsarin mulki ya ba ta don aiwatar da aikinta.

Ana zargin an sayar da filin da gwamnatin jihar ta bayar da shi a matsayin gudunmawa tun shekarar 1995 da farashin naira miliyan 400 kacal, duk da cewar an kimanta darajarsa da biliyoyin naira, lamarin da ya janyo bacin rai a tsakanin mambobin kungiyar Musabaqah.

Leave a Reply