‘Duk wanda ya samu damar lashe tikitin fidda gwani zan taya shi murna’ – Buhari

0 98

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fice daga wajen babban taron jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban kasar ya fice ne bayan ya gabatar da jawabinsa a wajen zaben fidda gwanin.

Kafin tafiyar sa, shugaba Buhari ya shaidawa ‘ya’yan jam’iyyar da su kasance masu hadin kai, kuma su guji tayar da zaune tsaye.

Ya kuma ce akwai bukatar jam’iyyar ta zabi shugabannin da za su ci gaba da dorawa akan ayyukansa na alkhairi.

Shugaban ya ce, dole ne wanda zai lashe zaben fidda gwanin ya zama mai ilimi, mai kishin kasa mai adalci mai tsananin imani da hadin kan kasa da karfin hali da manufa don ciyar da kasar gaba.

Ya taya murna ga wadanda tuni suka samu tikitin takara a jam’iyyar domin zaben 2023, ya kuma bukace su da su yi fice wajen cin nasara, musamman ga abokan takararsu da suka kayar a zaben fidda gwani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: