EFCC ta kama mutane 5 ‘yan kasar China masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Najeriya

0 100

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi ‘yan kasar China ne masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kauyen Ndito-Eka-Iba, a karamar hukumar Ibieno a jihar Akwa Ibom.

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Ya ce jami’an tsaro na musamman a kan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne suka kama mutanen a hukumar da ke Uyo.

Mista Oyewale ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan haramtattun kamfanonin hakar ma’adinai na kasashen waje a kananan hukumomin Eket da Ibieno na Akwa Ibom.

A cewar Oyewale Wadanda ake zargin za su fuskanci hukunci a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: