EFCC Ta Samu Nasara A Kotu Bisa Bukatar Kwace Gidaje 324 Domin Asusun Fanshon Ma’aikatan Jihar Kano

0 73

Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annti (EFCC) ta samu nasara a kotu bisa bukatar kwace gidaje 324 domin asusun fanshon ma’aikatan jihar Kano.

Mai shari’ah Inyang Ekwo ta Babbar kotun tarayya dake Abuja ce ta bayar da umarnin yayin da take yanke hukunci kan karar da EFCC ta shigar na neman kwace gidajen wadanda a cewar hukumar an mallake su ne daga kudaden da ake kyautata zaton an kwashe daga asusun fanshon ma’aikatan jihar Kano.

A cewar alkalin, gidajen sun kunshi gidaje guda 168 dake rukunin gidaje na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam na Bandirawo City a Kano da gidaje 122 dake rukunin gidajen Sheikh Nasiru Kabara a Amana City a Kano.

Sauran sune gidaje 38 dake rukunin gidaje na Sheikh Kalifa Ishaq Rabiu na Kwankwasiyya City a Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: