Gwamnatin Kano Tayi Alwashin Bawa Aisha Dorayi Gida Da Kudi Naira Miliyan Uku

0 81

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin bayar da sabon ginannen gida da kudi naira miliyan uku ga ‘yar asalin jihar, Aisha Abubakar Dorayi, bisa zama ta biyu a gasar karatun qur’ani ta shekarar 2022 wacce aka gudanar a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabwa.

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wannan alkawari a jiya yayin taron majalisar zartarwa ta jihar a gidan gwamnati dake Kano.

Ya ce an yanke shawarar baiwa wacce ta yi nasara kyauta shi ne domin a karfafa wa sauran ‘yan asalin jihar kwarin gwiwa ganin sun yi fice.

Da take jawabi bayan sanarwar bata kyautar, wacce ta lashe kyautar, Aisha Abubakar Dorayi daga karamar hukumar Gwale ta jihar ta yaba da wannan karimcin tare dayin alkawarin ci gaba kokarin.

Ta godewa iyayenta da malamanta da abokan aikinta da suka karfafa mata gwiwa wajen samun ilimi har zuwa wannan matakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: