Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kaduna ya maido da wutar lantarki a Birnin Kebbi sa’o’i kadan bayan gudanar da wani taro da gwamnatin jihar Kebbi.
Taron wanda ya gudana bisa umarnin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, an gudanar da shi ne a ofishin majalisar zartarwa domin warware rashin fahimtar juna da ke tsakanin kamfanin da sojojin kasarnan.
Sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri ne ya jagoranci taron da aka yi tsakanin kamfanin samar da wutar lantarki da shugabannin rundunar sojojin kasarnan da wasu shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
A halin da ake ciki kuma, zababben Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu, Garba Musa Maidoki, ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Dan-Ummaru Danko Wasagu a jihar kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 30 ciki har da ‘yan sanda biyar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Musa Maidoki ya jajantawa al’ummar jihar tare da addu’ar Allah ya jikan mamacin.