El-Rufa’i ya ƙalubalanci Ministan Tsaro kan zargin kitsa kisan Kudancin Kaduna
Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, sun bai wa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, wa’adin kwanaki bakwai da ya gabatar da hujjar zargin da ya yi wa tsohon gwamnan na cewa ya shirya kashe-kashen mutane a Kudancin Kaduna ko kuma ya janye kalamansa sannan ya ba da haƙuri.
Iyalan sun ce za su ɗauki matakin shari’a idan ministan ya gaza cika buƙatar cikin wa’adin da suka ba shi.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban ɗan tsohon gwamnan, Hon. Mohammed Bello El-Rufa’i, ya sanya wa hannu a madadin iyalan a ranar Litinin.
A cikin sanarwar, iyalan sun ce sun damu matuƙa da kalaman da Janar Musa ya yi yayin wata hira kai tsaye da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar 3 ga Satumba.
A yayin hirar, Ministan Tsaron ya zargi gwamnatin El-Rufa’i da raba Jihar Kaduna gida biyu, yana cewa mutanen Kudancin Kaduna sun sha fama da kashe-kashe da kuma wariya a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.
Musa ya ce: “Ba za mu taɓa farin ciki da mutumin da ya shirya kashe mutanenmu da gangan ba,” yana mai magana kan yadda wasu mazauna Kudancin Kaduna ke kallon tsohon gwamnan.
Ya kuma zargi El-Rufa’i da yin wasu kalamai da suka shafi biyan ’yan bindiga, tare da cewa akwai bidiyoyi da jawabai da za su iya tabbatar da zarge-zargen.
Sai dai iyalan tsohon gwamnan sun musanta zarge-zargen, suna cewa ministan bai gabatar da wata hujja a lokacin hirar da za ta tabbatar da cewa El-Rufa’i ya shirya kashe-kashen ba.
Sun ce idan Ministan ba zai iya gabatar da hujjar da yake da’awa ba, ya kamata ya janye kalamansa a kafar da ya yi su, wato Channels Television, sannan ya ba da cikakken haƙuri.
A cewar sanarwar, wa’adin kwanaki bakwai ya fara daga ranar 7 ga Satumba, inda aka buƙaci ministan ya gabatar da hujjoji ko kuma ya janye zargin.
Iyalan sun ce muddin wa’adin ya cika ba tare da an warware batun ba, za su ɗauki duk matakan shari’a da suka dace domin kare martabar tsohon gwamnan.
A wani mataki na daban, lauyoyin El-Rufa’i sun kuma aika wa ministan takardar gargadi kafin shari’a, inda suka nemi a janye zarge-zargen tare da neman diyya ta Naira biliyan 10 kan abin da suka bayyana a matsayin ɓata sunan tsohon gwamnan.