An kama ƙananan yara 43 masu safarar miyagun ƙwayoyi a Kano
An kama ƙananan yara 43 da ake zargi da shaye-shaye, sata da kuma safarar miyagun ƙwayoyi a wasu sassan birnin Kano.
Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaƙi da Shaye-shaye da Safarar Miyagun Ƙwayoyi, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce an kama yaran ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Sabon Gari, Gadar Lado, Unguwar Uku da Kofar Ruwa.
Ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya gano cewa wasu daga cikin yaran suna zama a tashoshin mota, ƙarƙashin gadoji da sauran wuraren taruwar jama’a, lamarin da ke sanya su cikin haɗarin faɗawa hannun masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Rimingado ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu manya ke amfani da ƙananan yaran wajen aikata laifuka, ciki har da kai saƙon miyagun ƙwayoyi da sata.
Ya bayyana cewa an riga an samu nasarar gurfanar da wasu manya biyu da ake zargi da ɗaukar ƙananan yaran aiki wajen safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin shekara tara ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Shugaban rundunar ya ce cikin kwanaki 40 da ta fara gudanar da ayyukanta, ta kai samame kusan 100 a wuraren da ake zargin ana aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, inda aka kama sama da mutane 200 tare da gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu.
Ya ce hukumomin sun kuma gano cewa da yawa daga cikin ƙananan yaran da aka kama sun fito ne daga jihohin Jigawa, Katsina, Zamfara da Adamawa.
Rimingado ya ƙara da cewa rundunar na shirin kama ƙananan yara masu shaye-shaye 2,500 cikin makonni biyu masu zuwa, yayin da take da shirin gano tare da taimaka wa manya 10,000 da ke fama da matsalar shaye-shaye a jihar.
Ya jaddada cewa yaƙi da shaye-shaye ba zai tsaya ga kama masu laifi kawai ba, yana mai cewa akwai buƙatar iyaye da sauran al’umma su ƙara kula da yara tare da taimaka wa hukumomi wajen kare su daga faɗawa cikin shaye-shaye da aikata miyagun laifuka.