’Yan Sanda Sun Ceto Yara 17 da Aka Sace A Kurmi

0 52

’Yan sanda sun ceto yara 17 da aka sace a Kurmi

’Yan sanda sun ceto wasu ƙananan yara 17 masu shekaru biyu zuwa bakwai da aka sace su a Jihar Oyo.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta ce ta kuɓutar da yaran ne daga waɗanda ake zargin sun sace su domin sayarwa ga bokaye da matsafa.

Wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen satar yaran da safarar su zuwa wasu sassan ƙasar nan sun shiga hannu, a cewar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo, CP Abimbola Ayodeji Olugbenga.

Ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Eleyele, Ibadan, babban birnin jihar.

Ya ce an ceto yaran tare da kama waɗanda ake zargin sun sace su a maɓoyarsu da ke jihohin Oyo, Ogun da Delta.

A cewarsa, ɗaya daga cikin mutanen aka kama, wata mata mai suna Adejoke Popoola, ta amsa cewa ta taɓa satar yara sama da 15 a wurare daban-daban na jihohin.

Kwamishinan ya ce binciken da ’yan sanda suka gudanar ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin suna satar ƙananan yaran ne daga coci-coci da kuma wuraren gudanar da bukukuwa.

Ya ce a garin Mowe da ke Jihar Ogun, an kama wata mata mai suna Adekanbi Jannet, inda aka ƙwato yara huɗu tare da wasu mata biyu masu juna biyu.

A Jihar Delta kuma, rundunar ta ƙwato yara huɗu daga hannun wasu mutane biyu, Christopher Joy, mai shekara 48, da Rosemary Jesse, mai shekara 53.

Ya ce ana zargin mutanen sun sato yaran ne daga Jihar Oyo domin sayar da su a Jihar Delta.

Kwamishinan ya ce daga cikin mutane bakwai da aka kama akwai wani mai suna Alfa Murtala Fasasi da kuma wani boka mai suna Yakubu Azeez, waɗanda ake zargin sun bayyana wa jami’an tsaro irin rawar da suke takawa wajen amfani da sassan jikin ƙananan yara domin tsafin neman kudi.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya yi kira ga iyayen da ’ya’yansu suka ɓace da su gaggauta kai rahoto ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo da ke Eleyele, Ibadan.

Leave a Reply