Kamfanin Dangote Ya Kaddamar da Sayar da Hannayen Jari Na Matatar Mai Na Naira Tiriliyan 2.15

0 68

Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da sayar da hannayen jari na matatar mai na Naira tiriliyan 2.15

Kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals ya sanar da shirin sayar da hannayen jari guda biliyan 4.1, a kan ₦525 kan kowane jari, wanda zai iya tara kusan ₦2.15 tiriliyan idan aka sayar da su gaba ɗaya.

Za a buɗe damar neman hannayen jarin daga 14 ga Satumba zuwa 14 ga Oktoba 2026, yayin da ake shirin saka hannayen jarin a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya (NGX) a watan Nuwamba.

Masu zuba jari za su iya fara shiga da hannu 10 kacal, wanda darajarsu ta kai ₦5,250. Kamfanin ya ce yana sa ran jawo hankalin kusan masu zuba jari miliyan 10, domin bai wa talakawa da ƙananan ’yan kasuwa damar zama masu hannun jari a matatar.

Babban jami’in kamfanin, Aliko Dangote, ya ce manufar sayar da hannun jarin ba tara kuɗi kaɗai ba ce, illa kuma faɗaɗa mallakar matatar ga ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka. Kuɗaɗen za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukan kamfanin, yayin da ake shirin ƙara ƙarfin tace man daga kusan ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.

Leave a Reply