Fursunoni 51 sun mutu bayan wata gobara ta mamaye wani gidan yari a kasar Pakistan

0 89

Fursunoni 51 sun mutu bayan wata gobara ta mamaye wani gidan yari mai cunkoso dake kusa da Jakarta babban birnin kasar Indonesia.

Gobarar a gidan yarin na Tangerang ta kama a daren yau lokacin da mafiya yawan fursunonin suke bacci. Masu gadi sun bude wasu dakuna amma sun tsere lokacin da wutar ta cigaba da ruruwa.

Wasu fursunonin kasashen waje biyu, daya daga kasar Portugal dayan daga Afirka ta Kudu, na daga cikin wadanda suka mutu.

Ministan doka da yancin dan adam na Indonesia Yasonna Laoly ta fada a wajen taron manema labarai cewa an sanar da ofisoshin jakadancin kasashen biyu.

Yace mutane 8 sun samu munanan raunkuka kuma karin wasu gommai sun samu kananan raunuka.

Wani faifan talabijin ya nuna hayaki ya turnuke saman gidan yarin daidai lokacin da wutar take ci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: