Uwar kungiyar yan jaridu ta kasa reshan jihar Jigawa ta aike da takardar yabo ga gidan Radiyon Sawaba FM dake Hadejia, takardar wacce ke dauke da kwanan watan 9/10/2020 da kuma sa hannun sakataren kungiyar Garba Muhammed Bulangu ta bayyana irin aiyukan kwarai da gidan Radiyon Sawaba yayi musamman a lokacin da ake fama da ambaliyar ruwa a yankin masarautar Hadejia.

“Mun samu labarin irin aikin alherin da kuka yi na kara lokacin shirye-shiryenku har a wanni 24h, da kuma rohoto kai tsaye a lokacin da abubuwan ambaliyar ke faruwa.”


“Babu tantama wannan yunkurin na sanarwa da al’ummar da suke sauraronku da halin da ake ciki yayi matukar taimakawa mazauna matasa wajen hada kai da kuma yin aiki tare don kare ruwa daga yin mummunar barna.”

Don haka ne “kungiyar yan jaridu reshen jihar Jigawa take yabo ga Sawaba FM da wannan hobbasa da kuma kokarin da kuke yi har ma da ragowar shirye-shiryenku cikin kwarewa da kuma bin dokar aiki.”

Saboda haka ne kungiyar ta bukaci Sawaba FM da ta cigaba da yin wannan kokari domin amfanin al’umma.

Jafaru Idris

Da yake nuna jin dadinsa da wannan shaidar yabo, shugaban gidan Radiyon Malam Jafaru Idris ya ce a madadinsa da duk sauran ma’aikata sun yi matukar murna kuma hakan zai kara musu kaimi wajen cigaba da aikin alherin da suke yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: