Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamitin tsakanin ma’aikatu wanda zai lalubo hanyoyin da za abi a rage barnar da ambaliyar ruwa ke jawowa a fadin kasarnan.
Ministar jin kai, kula da annoba da jin dadin jama’a, Sadiya Umar Farouq, wacce ta kaddamar da kwamitin a Abuja, tace kwamitin zai yi aiki tukuru wajen samar da wani shirin kasa na shiryawa annoba da bayar da tallafi.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Ministar tace hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta samar da hanyoyin kula da ambaliyar ruwa, kuma akwai shirin kai ziyara zuwa ga gwamnatocin jihoshi domin duba yadda aka shirya da kuma bayar da agajin ambaliyar ruwa.
Yace an zakulo yan kwamitin daga ma’aikatar jin kai, kula da annoba da jin dadin jama’a, da ma’aikatar da albarkatun ruwa da ma’aikatar gona da ta muhalli da ma’aikatar cikin gida da ta yada labarai, da sauransu.