Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Makarantar Sheikh Albani A Zariya

0 211

Wata gobara ta tashi a makarantar Sheikh Albani da ke Zariya a Jihar Kaduna, inda ta ƙone wani sashe na makarantar tare da haddasa asarar kayayyaki.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta shafi bangaren firamare na maza, sannan ta lalata ɗakin kwanan ɗalibai da wasu muhimman kayayyaki da ke cikin makarantar.

Jami’an kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka yi nasarar kashe wutar tare da hana ta bazuwa zuwa sauran gine-ginen makarantar.

A halin yanzu, ana ci gaba da tantance musabbabin tashin gobarar da kuma yawan asarar da ta haifar.

Hotuna: Ishaq Galadima

Leave a Reply