NEMA Ta Gargaɗi Al’ummar Jihar Jigawa Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa

0 227

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi gargaɗi ga mazauna wasu ƙananan hukumomi 17 na Jihar Jigawa da aka bayyana a matsayin yankunan da ke cikin matsakaicin haɗarin ambaliyar ruwa a daminar shekarar 2026.

A cewar bayanan da hukumar ta fitar, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Auyo, Birniwa, Birnin Kudu, Dutse, Guri, Gwaram, Jahun, Kafin Hausa, Kaugama, Kiri Kasama, Kiyawa, Malam Madori, Miga, Taura, Hadejia, Maigatari da Ringim.

NEMA ta shawarci al’umma da su ɗauki matakan kariya domin rage haɗarin ambaliya, ciki har da share magudanan ruwa, kauce wa zama a yankunan bakin kogi, da kuma gujewa gina gidaje a kan hanyoyin ruwa.

Hakazalika, hukumar ta gargadi jama’a da su guji tafiya ko tuka ababen hawa cikin ruwan ambaliya, su rika kai rahoton lalacewar magudanan ruwa ga hukumomin da abin ya shafa, tare da bin sanarwar gaggawa daga hukumomi domin kare rayuka da dukiyoyi.

Leave a Reply