A yanzu haka gonakin shinkafa na manoma fiye da dari bakwai ne suka salwanta a garin Zandam ta Gabas dake yankin Karamar hukumar Gwaram sakamakon ruwan kogi da ya mamaye gonakin.
Mai magana da yawun daruruwan manoman da iftila’in ya shafa kuma Sakataren kungiyar cigaban garin Zandam, Malam Ahmed Yakubu Zandam ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da wakilin mu.
Ya ce ballewar ruwan kogin ta haifar da hasarar shinkafa ‘yar rani da aka noma ta miliyoyin naira.
Malam Ahmad Yakubu Zandam ya kara da cewa ruwan kogin ya rufe gonakin manoma da yashi, lamarin da ya jefa manoman yankin cikin halin ha’ula’i, bayan manoman sun kashe makudan kudade wajen noman shinkafar.
Sakataren kungiyar ta cigaban garin Zandam daga nan ya roki gwamnatin jihar Jigawa da sauran hukumomin ba da agaji da su tallafa wa manoman da abun ya shafa domin rage musu dunbun hasarar da suka yi.